SiyasaJamus
CDU ta tsayar da wanda zai gaji Angela Merkel
April 12, 2021Talla
Jam'iyyar CDU ta Shugabar gwamnatin Jamus, ta goyi bayan aniyar shugabanta Armin Laschet ta neman kujerar shugabancin gwamnati a zaben kasa da za a yi cikin watan Satumba.
Sakataren jami'iyyar, Paul Ziemiak, ya ce Laschet ya sami goyon bayan mambobin jam'iyyar, da ma na wasu daga cikin 'yar uwar tagwaitakar CDU wato jam'iyyar CSU duk da cewa shugaban CSU Markus Soeder na neman matsayin shugabancin gwamnatin, mutumin da ya ce bai janye aniyarsa ba.
Sakataren jam'iyyar CDU Ziemiak, ya bayyana goyon bayan da Laschet ya samun ne dazu-dazun nan a lokacin wani taron manema labaru bayan matsayar da aka cimma a yau Litinin.