1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya:Rikici kan kudin kananan hukumomi

May 20, 2019

A wani abun da ka iya kai wa zuwa ga babban rikici a tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin Tarayyar Najeriya 36, kungiyar gwamnoni ta kasar ta ce ba ta yadda a bai wa kananan hukumomi damar sarrafa kudinsu ba.

https://p.dw.com/p/3ImMy
Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Kudin da aka tanada domin kananan hukumomi na shiga aljihun jihohiHoto: Getty Images

Kungiyar gwamnonin dai ta ce ba za ta sabu ba wai bindiga cikin ruwa, kokarin da hukumar kula da kudade ta kasar ke yi na karbe ikon sarrafa kudade na kanana na hukumomi na kasar daga hannu na jihohin ba. Babu dai zato ba kuma tsammani wani sabon umarni daga hukumar kula da shige da fice na kudade a cikin Tarayyar Najeriya ta ce ta haramtawa jihohi daukar ko kwandala daga kudaden kananan hukumomin da ke karkashinsu a halin yanzu. Hukumar dai ta ce duk wani bankin Tarayyar Najeriyar da ya hada baki da wani jami’i na gwamnatin jiha wajen fitar da kudin kananan hukumomi  to kuwa yana shirin fuskantar fushin hukumomin kasar, umarnin kuma da ke nufin zare ikon sarrafa dukiyar kananan hukumomin da jihohi suka dauki shekara da shekaru suna wadaka a ciki. To sai dai kuma tuni sabon umarnin ya harzuka jihohin kasar da ke fadin ba ta sabo wai bindiga cikin ruwa.

NO FLASH Nigeria Plastikflasche PET Flasche
Samar da atabtataccen ruwan sha ga al'ummar karkara na daga cikin ayyukan kananan hukumomiHoto: AP

Abdurazak Bello Barkindo dai na zaman kakaki na kungiyar gwamnoni ta kasar da kuma ya ce hukumar ta Nigerian Financial Intelligent Unit ta wuce makadi cikin rawa a umarnin nata. Hukumar NFIU din dai ta ce ta dauki matakin ne bayan tabbatar da neman karyewar tsari na hukumomi na kasar sakamakon kwashe kudaden raya kasa na kananan hukumomin, daga bangaren gwamnonin jihohin. Kusan Naira Triliyan 14 mallakar kananan hukumomin ne dai  ake ji sun shiga hannun jihohin kuma an kai ga kashe su, tun bayan wani hukuncin kotun koli na shekara ta 2002 da ya mallaka ikon tafi da harkokin kananan hukumomin a hannun jihohin. A fadar Sani Tukur da ke zaman kakakin hukumar ta NFIU, umarnin nasu na bisa kan hanya sannan kuma na da goyon bayan dokoki na kasar. Ana dai kallon takaddamar a matsayin son somi a cikin wani yunkuri a bangare na gwamnatin kasar na tabbatar da cikkaken 'yanci na kananan hukumomin da kundin tsarin mulkin kasar ya amince da kafa su, amma kuma jihohin kasar suka mai da su kango. Kusan sama da kaso 20 na makudan kudin Tarrayar Najeriyar ne dai ya kamata ya isa kanana na hukumomin da ke da alhakin kula da lafiya a matakin farko da ilimin firamare da ma ragowa na bukatu na mutane na karkara.