1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar ceto 'yan mata sama da 200 a Sambisa

Uwais Abubakar Idris/LMJApril 29, 2015

Masu fafutukar ganin an kwato ‘yan matan Chibok sun mayar da martani a game da bayanin da sojojin Najeriya suka fitar na kwato mata kusan 300 a dajin Sambisa.

https://p.dw.com/p/1FHY8
Kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Najeriya
Kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo

Sansanoni hudu ne sojojin Najeriyar suka ce sun samu nasarar 'yantar da su daga hannun kungiyar Boko Haram din wanda hakan ya basu damar ceto ‘yan mata har 200 da kuma manyan mata 93. Ceto wadannan mata dai ya samar da sabon fata ga ‘yan uwan ‘yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace sama da shekara guda ke nan. Bayanai sun sha ban-ban a kan zahiri ‘yan matan da aka ceto, ko akwai ‘yan matan Chibok din a cikinsu ko kuwa babu kasancewar rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ba ‘yan matan Chibok din bane, amma dai tana ci gaba da bincike don tan-tance su. Kanal Sani Usman Kuka Sheka shine mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar sojan Najeriya ya kuma yi mana karin haske yana mai cewa...

Halin da iyayen 'yan matan Chibok ke ciki
Halin da iyayen 'yan matan Chibok ke cikiHoto: DW/A. Kriesch

"Tan-tance 'yan matan da aka ceto

"Hakikanin gaskiya bincike da ake yi ya nuna basa ciki domin a yanzu haka ana ci gaba da tan-tance su domin a san daga ina suke kuma ana kai musu dauki."

Ko da aka tambaye shi yadda suka gane ba ‘yan matan Chibok din bane bayan ya ce suna kan tantanace su, Kanal Kuka ya ce...

"Eh dalili shine wasu daga cikin yaran na cewa 'yan Gwoza ne su. In Gwoza uka fito ya sunanku da sauransu, to dole ne ka tabbatar da abunda zaka sanarwa jama'a don ya kasance gaskiya ne''.

Sabon fatan ceto yaran Chibok

Kungiyar da ke fafutukar kwato ‘yan matan na Chibok ta Bring Back Our Girls dai na cike da fatan ganin an kaiga kwato su. Ko samun nasarar ceto wadannan mata kusan 300 ya samar da sabon fata a gare su? Mr Hosea Habana Tsambido shine shugaban kungiyar al'ummar Chibok da ke Abuja ya ce da wanda yace ba ‘yan matan Chibok a cikin matan da kuma wanda yace suna bincikawa tukuna duk magana daya ne, kana ba abu ne mai sauki da ga ceto su a gano ‘yan Chibok a ciki ba sai dai hakan ya zuba musu ruwa a zuciya kana sun ji sanyi.

Fafutukar kwato 'yan matan Chibok
Fafutukar kwato 'yan matan ChibokHoto: picture-alliance/dpa

A yanzu dai hankula sun karkata a kan hare-haren da sojojin ke kaiwa a dajin Sambisa da ke jihar Borno, kana abin jira a ganin shine ko wannan mataki na nuna kama hanyar cika alkawarin da gwamnati mai barin gado ta yi na cewa za ta gano ‘yan matan na Chibok kafin cikar wa'adin mulkinta a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.