Hare-haren Boko Haram a Chadi
April 16, 2019Kungiyar Boko Haram ta hallaka sojoji bakwai a wani harin da mayakan suka kai a kauyen Bouhama da ke yankin Tafkin Chadi a cewar wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar Chadi ta fitar. Ministan tsaro da shugaban hafsan hafsoshin soja sun kai ziyarar gane wa idonsu halin da yankin yake ciki. Sai dai sanarwar ta ce sojojin kasar Chadi sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram 63 a martanin da sojan suka mayar.
Yankin na Tafkin Chadi mai makwabtaka da Najeriya ya sha fama da hare-haren Boko Haram inda ko a watan Maris suka kashe soja 23 a wani harin da mayakan jihadin suka kai wa wani barikin sojan Najeriya da ke kan gabar Tafkin na Chadi.
Kungiyar kare hakin bil Adama ta kasa da kasa wato FIDH ta nuna damuwa da yadda hare-haren Boko Haram ke kara kamari musamman ma a Chadi, tana mai cewa kasar ta jima ba tare da ta fuskanci ire-iren harin mayakan da take fuskanta ba a baya-bayan nan, duk da kokarin kai dauki ga sojan Najeriya da sojojin kasar Chadi 500 suka kai wa takwaransu na Najeriya a karshen watan Fabrairun da ya gabata.
Rikicin na Boko Haram ya hallaka mutane akalla dubu 27 tare da haddasa ‘yan gudun hijira fiye da miliyan daya da rabi daga Najeriya zuwa makwabtan kasashe kamar Nijar da Kamaru da kuma Chadi.