1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin sulhu tsakanin gwamnati da 'yan tawaye

Mahmud Yaya Azare AMA
March 14, 2022

An soma tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Chadi da kungiyoyin 'yan tawaye, da zummar lalubo bakin zaren warware rikicin tsaro da na siyasa da ke addabar kasar.

https://p.dw.com/p/48SnD
Tschad | Mahamat Idriss Déby, Präsident des Übergangs-Militärrates (CMT)
General Mahamat Idriss Deby Hoto: Brahim Adji/Tchad Presidential Palace/AFP

Mutane 100 daga bangarorin siyasa da kabilu da sarakunan gargajiya da maluman addinai na Chadi ne suka halarci taron, sai dai wasu jagororin 'yan tawaye 84 daga kungiyoyin 44 ba su samu halartar taron ba saboda dalilan rashin samun cikakkun takaddun tafiya. Ana cike da fatan ganawar ta keke da keke tsakanin bangarori mabanbanta na kasar da za ta zama  tubalin fara cirewa 'yan kasar ta Chadi kitse daga wuta, kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Qatar Sultan Bin Sa'ad Almuraikhy ke fadi. 

"Ya ce kasar Chadi kamar sauran kasashe masu tasowa na fuskantar kalubalen ci gaban kasa wanda kuma ba zai taba samuwa ba muddin ba kwanciyar hankali a fannin tsaro da na siyasa da ma na tattalin arziki, saboda haka dole kowane bangare yayi bakin kokarinsa ya kuma sadaukar da kai don ganin wannan tattaunawar ta samar da zaman lafiya." 

Karin Bayai : Afuwa ga 'yan siyasa da 'yan tawaye

Äthiopien Eröffnung des Gipfeltreffens der Afrikanischen Union in Addis Abeba | Moussa Faki Mahamat
Moussa Faki Mahamat shugaban hukumar AUHoto: Giscard Kusema/Press Office Presidency of DRC

Firaministan kasar Chadi Albert Pahimi Padacké, ya gode wa kasar Qatar kan wannan dammar da ta samarwa 'yan kasar sa yana mai cewa "Wajibi ne muyi amfani da wannan lokaci da ma wannan damar da muka samu wajen ceton kasarmu a madadin sake nutsuwa cikin tarzoma da tashe-tashen hankula." 

Shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya bayyan cewa dole mahalarta taron su hakura da wasu daga cikin kudurorin da muradunsu, domin cimma kyakkyawar matsaya, a yayin da 'yan tawayen suka nuna aniyarsu ta shiga tattaunawar da suka siffantata da ta ayita ta kare, muddin kowane bangare zai sanya kishin kasa a zuciyarsa, tare da fatan gwammnatin Chadi da ta fara da nuna kyakkywar aniya ta hanyar sako musu kadarorinsu da aka kwace bayan an ayyana yi musu afuwa.

Karin Bayai : Juyin mulki da yakar ta'addanci

A watan Janairun da ya gabata aka sallami wasu daga cikin jiga-jigan 'yan siyasa da 'yan tawaye bayan dokar yin afuwa da aka cimma a watan Nuwamban bara, sai dai har yanzu ana tsare da wasu daga cikin yan tawayen a gidan kurkuku wadanda ke kan bakarsu ta kwatar iko da karfin tuwo a kasar. Ana saran idan aka kawo karshen tattaunawar sulhu za’a bude hanyar gudanar da zaben shugaban kasa a kasar.