Makomar yaki da ta'addanci a Sahel
January 26, 2022Marigaya Idriss Deby na Chadi da Ibrahim Boubakar keita na Mali da Mahamadou Issoufou na Nijar da Roch Mark Christian Kabore na Burkina Faso da kuma Mohamed Ould Abdel Aziz na Mauritaniya ne dai, suka kafa kungiyar G5-Sahel a shekara ta 2014 da nufin hada kai domin yakar ta'addanci a kasashensu. A tsawon shekarunsu na mulki tsofaffin shugabannin kasashen sun dasa da juna tare da yin aiki kafada da kafada, sabanin sababbin shugabannin da suka maye gurbinsu a kasashen. Wasu dai na ganin zama tamkar na 'yan marina da sababbin shugabannin ke yi, ka iya kawo cikas ga yaki da ta'addanci a yankin.
Sai dai Malam Moussa Aksar na ganin ta wani fannin akwai yiwuwar yaki da t'aaddancin ya yi tasiri a yanzu ta la'akari da yadda wuka da nama na tafiyar da mafiyawancin kasashen ya koma hannun sojoji. To amma a nasa bangaren Malam Alkassoum Abdourahmane mai sharhi kan harkokin tsaro a Jamhuriyar Nijar, na ganin akwai bukatar kasashen duniya su kare dimukuradiyyar Nijar idan har ana so yaki da ta'addanci a yankin ya dore. Kawo yanzu dai al'umma sun zura ido su ga yadda kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso za su koma kallon alkibla daya a fannin yaki da ta'addanci, bayan juyin mulki mafi yawancin kasahen da ke cikin rundunatr ta G5-Sahel.