Chaina na adawa da tallafin Amirka ga Taiwan
April 24, 2024Chaina ta koka kan sabon kunshin tallafin da kasar Amurka ta amince da shi wanda za a ware dala biliyan 8 a matsayin tallafin soji ga Taiwan. An ware tallafin ne da nufin habaka bangaren tsaron tsibirin na Taiwan da ma inganta kayan yaki domin shirin ko ta kwana ga mamayar Chaina.
Ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta ce, karfafa alakar tsaro a tsakanin Amirka da Taiwan ka iya haifar da barazanar yaki.
Karin bayani: Majalisa dattijan Amirka ta amince da kudurin tallafi
Chaina dai ba ta dauki Taiwan a matsayin kasa mai cin gashin kanta, sai dai a matsayin lardin da ya balle kana yake neman 'yan ci kai daga kasar.
Hakan ya sanya shugabannin kasashen yammacin Turai da kuma na Amirka ke nuna damuwar ta yiwu Chaina ta iya amfani da karfi wajen kwace iko da Taiwan nan da shekaru masu zuwa.