China da Philippines na nuna wa juna dan yatsa
October 22, 2023Wani jirgin ruwa da ke tsaron gabar ruwan China ya yi taho mu gama da wani jirgin dakon kaya da dakarun sojin Philippines suka bayar da kwangilar kai abinci da sauran kayan bukatu ga dakarun da ke tashar Thomas Shoal, inda gwamnatin Beijing ke ikrarin nan ma yankin ruwanta ne.
Gwamnatin Philippines dai ta zargi masu tsaron tekun Chinar da alhakin aukuwar lamarin inda ta ce jiragen ruwan China ba su mutunta yarjejeniyar MDD na dokar kan teku ba.
To sai dai masu gadin tekun China sun zargi dayan bangaren da kutsa kai cikin ruwan China wanda hakan ya sabawa dokar kasa da kasa kan kaucewa cin karo a teku.
Karin bayani: Tada jijiyoyin wuya tsakanin China da Philippines
Kasashen biyu na na ci gaba da nuna juna dan yatsa kan yankin ruwan. Kasar Amirka da ta dade ta na dasawa da Philippines ta yi tir da matakin China.