1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China ta daure mutum 15 bayan ruftawar wani gini

October 17, 2024

Ginin da ake amfani da shi wajen kasuwanci ya rufta ne tare da halaka gomman mutane a watan Afrilun 2022.

https://p.dw.com/p/4ltRr
Hoto: Carlos Garcia Rawlins/REUTERS

Kafar yada labaran China ta ce gwamnatin kasar ta daure wasu mutum 15 da ke da hannu a gina wani katafaren gini da ya rufta kan gomman mutane a kasar.

A watan Afrilun 2022 ne wani gini da ake amfani da shi wajen cinikayya ya rufta kan jama'a a birnin Changsha na tsakiyar kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar sama da mutum 50 tare da jikkata wasu tara.

Karin bayani: Guguwar Yagi ta yi ta'adi a Vietnam da China

Daga bisani hukumomi sun bayyana cewa ba a bi ka'ida ba wajen yin ginin, abinda ya jawo cece-kuce kan cin hanci da rashawa a harkar gine-ginen kasar.

Kafar yada labaran China CCTV ta ce wasu kotuna biyu a birnin na Changsha sun yanke hukunci kan mutum 15 da ke da hannu a faruwar al'amarin.

Karin bayani: Sojojin China na gagarumin atisaye kusa da Taiwan

Wasu daga cikin mutanen da hukuncin ya shafa kamar  Wu Zhiyong mazauni a inda ginin ya rufta zai shafe shekara 11 a magarkama.