Ci gaba da luguden wuta a Gaza ka iya zama laifukan yaki
November 2, 2023Hakan na zuwa ne bayan wani sabon hari da dakarun Isra'ila suka kai karo na biyu a babban sansanin 'yan gudun hijira da ke Jabalia.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antoniyo Guterres ya bayyana matukar damuwa kan ruwan bama-bamai da dakarun Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza duk da kiraye-kirayen neman a tsagaita wuta.
Karin bayani: Isra'ila ta yi watsi da tsagaita wuta a Gaza
Sai dai Isra'ila ta ce sojojin nata sun kai harin ne ga mayakan Hamas, wani shaidun gani da ido ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP munin wannan harin a sansanin da mutane ke neman mafaka.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana cewa tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da martanin ramuwar gayya, ya zuwa yanzu Falasdinawa sama da mutum 8,700 ne suka mutu, mafi akasarinsu mata da kananan yara.