1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Netanyahu: Ba za mu tsagaita wuta ba

Abdullahi Tanko Bala
October 31, 2023

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da kiraye kirayen tsagaita wuta da Hamas yayin da sojojin Israila ke ci gaba da fadada farmaki ta kasa.

https://p.dw.com/p/4YDi2
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: imago images/Xinhua

Netanyahu ya ce kiran tsagaita wuta tamkar kira ne ga Israila ta mika wuya ga Hamas ta yi saranda ga ta'addanci, kuma hakan ba zai taba yiwuwa ba.

Ya yi kira ga kasashen duniya su bukaci sako dukkan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su ba tare da wani jinkiri ba.

Karin Bayani: Babban Zauren MDD na tattauna rikicin Gaza

A waje guda kuma shugaban hukumar jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinawa Phillipe Lazzarini da yake jawabi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya ce halin da ake ciki a Gaza yanayi ne na rai kwakwai mutu kwakwai wanda lallai ke bukatar a tsagaita wuta. Ya soki lamirin Israila na azabtar da daukacin Falasdinawa da tilasta tagaiyarar fararen hula.

A cewar alkaluma daga ma'aikatar lafiya ta Gaza yawan mutanen da suka rasa rayukansu ya haura mutum 8,300 yawancinsu mata da kananan yara.

Shugabar asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF Catherine Russell ta ya ce yara fiye da 3,400 aka kashe yayin da wasu fiye da 6,300 suka sami raunuka.