Ci gaban suka ga ziyarar Jonathan a Bornon Najeriya
January 16, 2015Wannan ziyara ta shugaba Jonathan wacce ita ce irin ta biyu da shugaban ya ziyarci yankin tun lokacin da aka fara samun matsalar tabarbarewar tsaro a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya da ta haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan Najeriya.
Yawancin wadan da suka tattauna da wakilin DW daga yankin sun bayyana bakin cikin su da wannan ziyarar da shugaban ya kai inda suka danganta ta da siyasa musamman ganin babu wani abu mai muhimmanci da shugaban ya bayyana in banda romon baka da ya yi musu.
Duk da cewa fadar gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa da ke nuna cewa ziyar ta nuna tausayawa tare da yin jaje ne. Yawancin ‘yan Najeriya musamman mazauna shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya na ganin ba za a iya rabata da yakin neman zaben da ke tafe ba.
Ga al'ummar jihar Borno da kuma jihohi makwabta, wannan ziyarar ba ta kulla musu komai ba don kuwa babu wani abu sabo da shugaban ya bayyana da zai nuna cewa gwamnatinsa na shirin magance matsalar da ta addabi yankin da ma Arewacin Najeriya baki daya.
Shugaban dai bai ce komai da za a iya cewa zai kwantar wa iyayen wadan nan ‘yan mata na Chibok hankali ganin har yanzu basu san halin da ‘ya‘yansu ke ciki ba.