Cikas a aikin shunfuda bututun iskar gas zuwa Turai
February 2, 2024A shekarar 2016 ne Najeriya ta cimma yarjejeniya da wasu kashashen Afrika da Turai kan aikin samar musu da makamashin iskar gas. Kasashen Afrika 12 da Spain wadda daga nan ne gas zai kwaranya zuwa wasu kasashen na Turai ne suka amince da wannan aiki da zai ci kimanin dala biliyan 25 na Amurka. Wannan aiki da ake ta maganarsa a ciki da wajen Najeriya tun tsawon lokaci, an nunar cewa yana da mahimmancin gaske, duba da kimimin kudaden shiga da za su fado lalitar Najeriyar, da kuma yadda samar da gas zai cike gibin da kasar Rasha ta haifar a nahiyar Turai sakamakon rikicinta da kasar Ukraine.
Karin bayani: Karin iskar gas daga Najeriya zuwa Turai
Mr Kofi Bartel, masani a harkokin mai da Gas a yankin Niger Delta ya ce: " Najeriya na kan gaba a yawan makamashin gas a duniya domin tana dauke da kaso uku na gas da ke duniya, kuma ko da yake tana da wannan arziki, matsalolin shekaru da dama sun hana ta katabus kan harkar ta gas."
Tun farko, masana sun ta ankarar da Najeriya wacce ita ce za ta samar da wannan gas kan bukatar tsayawa tsaye wajen ganin an tantance batutuwan da suka shafi wannan yarjejniya da kuma alfanun da za ta samar. Masanan na ganin cewar ba a kai ga yin hakan ba, face wata rufa-rufa da ke ci-gaba da zaike wa aikin. Duk da shan alwashin da Najeriya ke yi na rashin tsaiko a wannan aiki, amma akwai kalubale na samar da isasshen sinadarin gas da Najeriya za ta yi amfani da shi wajen sarrafa iskar gas da za ta fidda wadannan kasashe,don haka akwai matsala.
Karin bayani: Rub da ciki da kuɗaɗen mai da iskar gas a Najeriya
Masana a harkokin danyan mai da makamashin gas da wasu jami'ai na manyan kamfanonin sarrafa mai da gas na kokawa kan yadda Najeriya ta gaza kammala shumfuda bututun gas a sassan kasar, kamar yadda a ka tsara tun shekaru baya, ballanta na a mayar da hankali kan shumfuda bututun gas na tsawon kilomita 5300 daga Najeriya zuwa Maroko, su kuma tike a Turai. Najeriyar ce ke zaman ta tara a duniya a arzikin na makamasnin gas.
Karin bayani: Man Najeriya na tagomashi a kasashen Turai
An dai tabbatar da cewar,karancin kudaden aiwatar da ayyukan sarrafa makamashin na gas,da matsalar ambaliyar ruwa kan turbar da bututun Gas za su bi,da ma wasu matsaloli na cikin gida, gami da na tsaro sun zama dalilin dabaibayi ga harkokin na gas a Najeriya. Wannan yanayi ya sa kasar ta kasa zamowa tagomashin da ya kamata a kasuwar makamashin gas ta duniya.
Karin bayani: Najeriya: Hauhawar farashin makashin gas ta jefa mutane cikin mawuyacin hali
Babban batu shi ne na yadda Najeriyar ta fara katafaren aikin, saboda rashin cimma wannan manufa na iya afkar da kasar cikin sarkakkiyar shari'a kan tuhumar wasa da hankula. Amma idan wannan katafaren aiki ya kai ga nasara, akwai yiwuwar ceto Naira wadda yanzu darajarta ta zamo abin dariya a duniya.