1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janye wa'adin korar fulani

Uwais Abubakar Idris ZAM
January 26, 2021

Yarjejeniyar sulhun da aka cimma a tsakanin kungiyar Fulani makiyaya da gwamnonin jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya na janye wa’adin fulanin su fice daga yankin na cigaba da daukar hankali.

https://p.dw.com/p/3oRKP
Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Cimma wannan yarjejeniya dai ya yayyafawa wannan matsala ruwan sanyi da ma kama hanyar samun zaman lafiya a tsakanin Fulani makiyaya da abokan zaman na su a  jihohin kudu maso yammacin Najeriyar na ‘yan kabilar yarabawa, bayan tashin tashina da batun ya haifar.

Sai da kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi takakka zuwa yankin kafin cimma wannan. Doki da murna da ya biyo bayan kaiwa ga cimma wannan matsaya da yanzu ya dushe kaifi na tada jijiyar wuya a tsakanin bangarorin Najeriyar dai muhimmi ne.

Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Ko kunyar ta Miyatti Allah da ke wakiltar mafi yawan fulanin Najeriya  na tunanen yarjejeniyar da suka cimawa ta hana kiwo da dare da sanya yaran da basu mallaki hankalinsu ba zuwa kiwo zasu kawo zaman lafiya.

Sanin cewa  muhimmin batu a rikicin shi ne na zargin matsalar garkuwa da jama'a a tsakanin bangarorin biyu na Fulani makiyaya da al'umman yankin Kudu maso yammacin Najeriya shi ne babban dalili na wannan matsala, ko za'a ce yarjejeniyar ta zama kamalalliya da za ta iya shawo kan matsalar.

Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Ana cike  da fatan cewa yarjejeniyar za'a fada irin wannan yarjejeniya zuwa sauran sassan Najeriya domin samar da zaman lafiya a tsakanin Fulani makiyaya da abokan zamansu domin komawa wancan yanayi da ake zaune cikin kwanciyar hankali da lumana da ma amfanar juna don ci gaban Najeriya.