Fargaba a iyakar Ruwanda da Yuganda
March 6, 2019Ministan harkokin wajen kasar Ruwanda Richard Sezibera ya musanta bayanin cewa kasar ta rufe iyakokinta da kasar Yuganda da cewa aiyukan gyaran hanya ne suka janyo wannan tsaikon. Duk da haka 'yan kasar Yuganda na ci gaba da shiga kasar Ruwanda amma gwamnatin Ruwanda ta hana 'yan kasarta da kayayyakin kasar shiga Yuganda. Ministan harkokin wajen Ruwanda ya ce tun da dadewa suke fuskantar matsaloli da Yuganda inda sun yi iya kokarinsu na ganin an daidaita amma abin ya ci tura.
Duk da cewa 'yan kasar Yuganda na da izinin shige da fice amma an sami wasu direbobin manyan motoci da suka makale a bakin iyakar kasar tun bayan rufe iyakar.
Da yawan 'yan kasuwa da ke sana'oinsu tsakanin kasashen biyu na kiran gwamnati da babbar murya da ta gagauta kawo karshen wannan matsalar. Diane Umwiza 'yar asalin kasar Ruwanda ce da ta makale a bakin iyakar kasar dauke da kayan siyarwa da take da nufin shiga kasar Yuganda ta ce ita da abokan huldarta na cikin damuwa.
Jama'ar kasar Ruwanda da ke da 'yan uwa da abokan arziki da abokan hulda kasuwanci na ci gaba da jiran gawon shanu, amma suna fatan shuwagabannin biyu da aka sani da kyakkyawar alaka za su hau teburin sulhu nan ba da dadewa ba.