COP28: Tattauna yarjejeniyar makamashi
December 11, 2023Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci samun masalaha yana mai cewa tushen nasarar taron na COP28 zai dogara ne a kan ko za a iya cimma yarjejeniyar rage amfani da makamashin kwal da man fetur da kuma gas cikin hanzari domin kauce wa mummunan bala'in sauyin yanayi.
Karin Bayani: Taron Cope 28 zai bai wa kasashe matalauta kudade
Guterres ya nanata kiran da kasashe masu tasowa suka yi cewa dukkan wani mataki na sauyin tsarin amfani da makamashi na duniya da za a cimma wajibi ne ya hada da tallafin kudi domin taimaka musu aiwatar da shi.
Hadakar kasashe fiye da 100 da suka hada da masu arzikin mai da iskar gas da Amurka da Kanada da Norway da kuma kungiyar tarayyar Turai kana da kasashen da ke kan tsibiri wadanda ke fuskantar barazanar sauyin yanayi suna bukatar yarjejeniyar da za ta fayyace kalamai karara na daina amfani da makamashin da ke fidda hayaki wanda kuma ke gurbata muhalli, abin da ba a taba cimma wa ba a shekaru talatin na taron kolin Majalisar Dinkin Duniyar kan sauyin yanayi.