Corona: An gurfanar da mutane 149 a Legas
April 17, 2020Talla
Wata sanarwa da rundunar 'yan sanda Legas din ta fidda wadda ke dauke da sa hannun kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi, ta ce wadanda aka gurfanar din sun aikata laifukan da suka hada da kisan kai da fashi da makami da kuma fita kan tutina don yin harkokinsu duk kuwa da dokar hana fita da aka kafa.
Tuni dai kotu ta bada umarnin tsare mutanen a wajen 'yan sanda har zuwa wani lokaci nan gaba inda kotun za ta sake zama ta cigaba da sauraron karar da aka gabatar.
Jihar Legas dai ita ce kan gaba a yawan mutanen da ke dauke da cutar ta Covid-19 kuma tun bayan da aka sanar da sanya dokar hana fita, mazauna birnin suke korafi na karuwar aikata manyan laifuka.