Coronavirus na kara bunkasa, inji WHO
February 28, 2020Talla
Mai Magana da yawun Hukumar Christian Lindmeier ya shaida wa 'yan jarida a birnin Geneva cewa da alama cutar na da karfin mamaye kusan kasashen duniya.
A gefe guda kuma kwamishinan lafiya na jihar Legas ta Najeriya Akin Abayomi ya ce dan kasar Italiya da aka samu da Coronavirus a Najeriya ya fara ratsowa ta kasar Turkiyya, a sa'ilin da ya iso Najeriya kuma sai da ya yada zango a jihar Ogun kafin daga karshe a gano yana dauke da cutar a wani asibitin da ke unguwar yaba ta birnin Legas a kudu maso yammacin Najeriya.