1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya kulle Kano

April 28, 2020

Wani sabon jawabi da shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi game da annobar COVID-19, da kuma ya mayar da hankali kan halin da ake ciki a jihar Kano, ya janyo mayar da martani cikin kasar.

https://p.dw.com/p/3bVzb
Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (dama) da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje (tsakiya) lokacin yakin neman zabe a KanoHoto: Salihi Tanko Yakasai

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dai, ya fito ne da nufin kwantar da hankalin al'ummar Tarayar Najeriyar da idanuwansu ke dada budewa da barazanar annobar mai tasiri a cikin kasar. Tun ba a kai ga ko'ina ba dai al'ummar sun fara mayar da martani ga jawabin da ya ambato sassautawa a biranen Legas da Abuja da jihar Ogun, sannan da kara tsaurin matakai a jihar Kano da ke neman rikidewa ya zuwa cibiya ta cutar a kasar.

Kyakkyawan fata

Faruk B B Faruk na zaman wani mai sharhi a cikin harkokin mulki na kasar, ya kuma ce tsarin da shugaban kasar ke dauka na kama da kwaiwayon Turawan da ke da arziki na tunkarar annobar a cikin sauri. Ga Hashim Sule da ke shirin tunkarar wasu makonni guda biyu a birni na Kano, akwai sabon fata a kalaman shugaban kasar.

Tricycles
Kano: Birni mai tarin jama'aHoto: DW/N. Zango

Ra'ayi dai ya bambanta tsakanin likitoci da ke tunanin karbe yakar cutar a hannun gwamnatin jihar da kuma masanan da ke ganin a kyale gwamnan ya taka rawa, na iya tasiri a kokari na tunkarar rikicin.

Hada hannu ko karbewa?

Dr. Husaini Tukar Hassan na zaman wani masani a cikin harkokin mulki, a cewarsa akwai bukatar shugaban kasar ya hada hannu da gwamnatin jihar domin warware batun. To sai dai ga Dr. Mohammed Adamu Askira da ke zaman wani likita a Kanon, karbe yakin daga hannu na jihar kadai ne zai iya taimakawa wajen kaucewa tunkarar annoba mai girma

Ya zuwa ranar yau dai yawan masu dauke da cutar ya tasamma 1,500 a  daukacin Najeriyar, a yayin kuma da asara ta rayuka ta kai 40.