1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba tarawi da tafsiri yayin azumi a Najeriya

April 21, 2020

A karon farko a cikin tarihin Musulunci na shekaru ba adadi, kungiyar Jama'atul Nasarul Islam ta Musulmin Tarayyar Najeriya, ta ce ba za a yi sallar tarawi da tafsiri a lokacin azumi ba saboda annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3bEK5
Nigeria Ramadan
Bana ba za a yi sallar jam'in tarawi da tafsiri lokacin azumi a Najeriya baHoto: picture-alliance/AA/M. Elshamy

Sallar tarawin ta nafila da tafsiri a lokacin azumin watan Ramadana dai, na zama na al'ada. Ba dai kasafai komai karfin 'yan mulki ke iya yanke hukunci a bisa batun addini a cikin Tarayyar Najeriyar kasar da ke takama da tisirin addin a tsakanin al'umma ba. To sai dai kuma daga dukkan alamu annobar COVID-19 tai nasarar mai da harkokin addinin ya zuwa baya, cikin kasar da ke fuskantar azumi da kuma ake shirin jingine al'adu na  lokacin  azumin.

Babu tarawi babu tafsiri

Wata fatawar  kungiyar Jama'atul Nasarul Islam  ta Musulmin Najeriyar dai, ta ce a bana kuma a karon farko da hankali zaya tuna, Musulmin kasar ba zasu gudanar da ibadojin al'ada na lokacin azumin a cikin bainar jama'a ba, da nufin kaucewa yada annobar cikin kasar.
Farfesa Ibrahim Maqari na zaman daya a cikin malamai guda 10 da suka jagoranci fatawar da ke zaman irinta ta farko da kuma ke iya tasiri a cikin harkokin addini a kasar. To sai dai kuma  fatawar daga dukkan alamu na shirin hada kan daukaci na kungiyoyi na musulmi na kasar, da a baya ke rabe bisa banbanci na  akida a tsakaninsu. 

Massen-Trauung in Nigeria
Babu zaman tafsiri a MasallataiHoto: Aminu Abubakar/AFP/Getty Images)

Hadin kan mabiya akidu

Dr Bashir Umar dai na zaman babban limami a masallacin Alfurkan da ke Kano, kuma a tunaninsa fatawar ta yi dai-dai, tun da dai al'adar ba ta  kai girman rai a cikin tsarin addini ba. Haka shi ma Ustaz Husaini Zakariya da ke zaman wani mai tafsirin a Masallacin Banex da ke Abuja fadar gwamnatin Njaeriyar. Tuni dai wasu malaman kasar suka dau hanyar kafafe na zamani da nufin isar da sakon da al'ummar kasar suke da bukata, a cikin sabon yanayin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.