Najeriya ta yi watsi da maganin COVID-19
July 3, 2020Najeriyar dai ta dauki lokaci mai tsawo tana bincike a kan maganin da kasar Madagaskar ta bai wa kasar kyauta domin shawo kan cutar sarkewar numfashin ta COVID-19, inda bayan bincike na kimiyya aka fitar da sakamako na sinadaran da ke cikin magani da aka ce yana cike na sinadarai na Tazargade. Tun a ranar 16 ga watan Mayun wannan shekarar ne dai, Najeriya ta karbi maganin cutar coronavirus din daga kasar Madagaskar, inda kuma nan take shugaban kasar ya yi alakwarin za a gudanar da bincike na kimiyya.
Tuni dai 'yan Najeriyar da suka sa ran samun sauki ta hanyar kokarin da ake ganin Madagaskar ta yi, suka fara mayar da martani a kan sakamakon binciken kimiyyar da aka gudanar din. A yanzu dai kallo ya sake komawa sama musamman ga kasashen Afirka, na su jajirce domin nemo maganin COVID-19 din, ba wai zura idanu na zaman tsammanin samun mafita daga kasashen da suka ci gaba ba, duk kuwa da cewa fiye da rabin wadanda suka kamu da cutar a Afrika sun warke.