COVID-19: Najeriya za ta karbo rance
April 6, 2020Talla
Najeriya ta bukaci rancen kudade ne da suka kai dala miliyan dubu shida da 900 da ta ce za ta yi amfani da su wajen yaki da annobar coronavirus.
Minstar kudin kasar Zainab Ahmed, wadda ta bayyana bukatar kudaden yau a Abuja, ta ce kasar za ta ranto kudaden ne daga Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni na duniya IMF, da ma bankin bunkasa kasashen Afirka, wato Afrcian Development Bank.
A cewarta kasar za ta karbo dala miliyan dubu uku da miliyan 400 ne daga bankin duniya, sai asusun IMF dala miliyan dubu biyu da miliyan 500, sai kuma dala biliyan guda daga bankin raya kasashen na Afirka.
Mutum 232 ne dai aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan kasar daban-daban, wasu biyar din kuma suka mutu da ita.