1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta taimakawa masana'antu

May 12, 2020

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ware Naira biliyan 50 domin farfado da masana'antun kasar, bayan da suka samu koma baya sakamakon annobar cutar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3c8Oa
Nigeria Gebäckproduzent Beloxxi
Tallafi ga masu masana'antu a NajeriyaHoto: DEG

Najeriya kasa ce mai cike da dumbin arzikin kasa. Sai dai annobar coronavirus da ta mamaye duniya ta shafi wannan fanni, wanda hakan ya tilastawa gwamnati daukar matakin da ya dace. Gwamnatin dai ta shirya domin bayar da tallafi da ya kama daga kan Naira miliyan uku zuwa 25 ga masana'antun kasar. Shi kuwa darakta janar na kungiyar masu masana'antu na kasar Mr Ambrose Uche ya koka ne kan yadda ake samun karin kudin ruwa a bankunan kasuwancin kasar. 

Ita kuwa madam Adah Mathew shugabar wani karamin kanfani a Lagos cewa ta yi: 
Akwai bukatar ganin an dagawa mutane kafa na tsahon shekara guda, dangane da bashin da za a biya gwamnati domin samun kwarin guiwa.
Hajia Rahma Aliyu ta kammala karatunta sama da shekaru 10 amma ba ta samu aiki ba, ta ce ta sha cike takardun tallafin gwamnatin, amma ba ta gani a kasa ba. A nasa bangaren, Alhaji Ibrahim Mustafa Tofa mai sharhi ga alamurran daya shafi kasa cewa ya yi ta hanyar kungiyoyi ne kawai 'yan kasuwar za su iya samun wannan tattalfin.