1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

An samu bullar cutar Coronavirus a Najeriya

Ramatu Garba Baba SB
February 28, 2020

Mahukunta a jihar Lagos da ke Najeriya sun tabbatar da cewa an samu cutar nan mai kama numfashi da aka yi wa lakabi da Covid-19 inda kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana.

https://p.dw.com/p/3YZUH
Coronavirus SARS-CoV-2 im Elektronenmikroskop
Hoto: picture-alliance/AP/NIAID-RML

Cutar nan mai kama numfashi da aka yi wa lakabi da Covid-19 ta bulla a Najeriya, Kwamishinan lafiyan jihar Akin Abayomi ya ce mutumin da aka gano da kwayar cutar, wani dan asalin kasar Italiya ne da ya shigo jihar daga birnin Milan a makon da ya gabata.

Tuni aka killace shi inda jami'an lafiya ke ci gaba da sa ido a kan mutumin. Birnin da shi ne mafi girma a nahiyar Afirka ya kasance cibiyar hada-hadar kasuwanci da ke hada kan jama'a daga sassan duniya. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke tsaka da matakan ganin ta hana bullar cutar a kasar mai yawan al'ummar da suka zarta miliyan 160.

A daya bangaren kuma, kasar New Zealand da Belarus sun tabbatar da labarin bullar cutar a kasashensu. Mutum fiye da dubu biyu da dari biyar Coronavirus ta halaka tun bayan bullar ta a Disambar bara.