1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta janyo hargitsi a kasar Gini

August 30, 2014

Wata zanga-zanga dangane da Ebola a kasar Gini ta jikata mutane da dama

https://p.dw.com/p/1D4BP
Liberia Ebola (Bildergalerie)
Hoto: Getty Images

Arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a kasar Guinea, inda ke zaman mafarin barkewar cutzar Ebola a yankin yammacin ya kai ga jikatar fiye da mutane 50, bisa bayanan da majiyoyin gwamnatin kasar suka bayar.

An dai sanya dokar hana fita a birnin Nzerekore, birnin mafi girma a mataki na biyu a kasar bayan da 'yan kasuwa suka kwashe Alhamis da Jumma'a suna zanga-zanga, saboda gwamnati ta tura ma'aikatan lafiya su yi musu feshi a kasuwa ba tare da sun sanar da su a kan lokaci ba.

Gwamnan yankin Lancei Conde ya tabbatar da cewa akwai jami'an gwamnati 27 daga cikin wadanda suka yi raunin. Abubakar Camara mai kula da lamura a birnin ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, masu zanga-zangar sun lalata wata motar asibiti da ma wasu motoci na asusun kula da yara ta UNICEF. Al'ummar wannan birnin dai ta kai yawan dubu 300 a 'yan shekarun baya-bayan nan sakamkon karuwan 'yan gudu hijirar da ke tserewa yakin basasa a kasashen Saliyo da Laberiya.

Fiye da mutane 1500 suka hallaka daga cutar ta Ebola kawo yanzu, a kasashen Saliyo, da Laberiya, da Gini, da kuma Najeriya a yayin da kasar Senegal ta sanar da samun wani mai dauke da cutar a karon farko, ranar Jumma'ar da ta gabata.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Suleiman Babayo