1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta kawo hargitsi a Laberiya

August 20, 2014

'Yan sandan ƙasar Laberiya sun yi amfani da hayaƙi mai saka hawaye kan masu zanga-zamga bisa cutar Ebola

https://p.dw.com/p/1CyB2
Hoto: Reuters

A wannan Laraba 'yan sandan ƙasar Laberiya sun yi amfani da hayaƙi mai saka hawaye kan dubban mutanen da ke zanga-zangar neman ficewa daga yankunan da aka killace domin hana yaɗuwar cutar Ebola, kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar.

A jiya Talata mahukuntan ƙasar suka kafa dokar hana fita ta ƙasa saboda neman daukan matakan yaƙi da cutar ta Ebola. ɓarkewar cutar ta yi sanadiyyar hallaka mutane fiye da 1,200 a ƙasashen Gini, da Saliyo, da Laberiya, da kuma Najeriya inda mutane biyar suka mutu. A wani labarin rahotannin daga Burma, sun ce ana gudanar da gwaji wa mutane uku bisa cutar ta Ebola, waɗanda suka fito daga ƙasashen na yammacin Afirka da aka samu ɓullar cutar ta Ebola.

Mwallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane