Cutar Kwalara ta halaka mutane da dama a Najeriya-NCDC
October 8, 2024Rahoton na NCDC na nufin cewa an samu karin kaso 239% na adadin mutanen da suka kamu da cutar a watanni taran farko na shekara ta 2024 a fadin kasar. Hukumar ta ce mutane 359 sun mutu daga watannin Janairu zuwa Satumbar wannan shekara, idan aka kwatanta da mutane 106 da suka mutu a shekara ta 2023.
Karin bayani: Cutar Lassa ta halaka mutum 110 a Najeriya
JIhar Legas ce ke kan gaba na yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ta amai da gudawa da galibi ake dauka ta ta'ammali da ruwan sha mara tsafta, a cewar NCDC. Kazalika hukumomin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun sanar da barkewar annobar ta kwalara a jihar sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa jihar, wanda hakan ya raba mutane sama da miliyan biyu da muhallansu.