1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwamnatin Borno ta sanar da bullar amai da gudawa

October 4, 2024

Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da rahotannin bullar annobar amai da gudawa 451 a kananan hukumomi biyar daga cikin 27 da ke fadin jihar.

https://p.dw.com/p/4lQsR
Masu aikin ceto a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno a Najeriya
Masu aikin ceto a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno a NajeriyaHoto: Audu Marte/AFP

Kwamishinan lafiya na jihar Borno Farfesa Baba Malam Gana shi ne ya sanar da barkewar cutar ta kwalara, inda ya ce mutane 451 ne suka kamu da wannan cuta a kananan hukumomin Jere da Mafa da Konduga da Dikwa da karamar hukumar birnin Maiduguri da ke murmurewa daga ibtila'in ambaliyar ruwa da ya yi sanadiyyar rayuka.

Karin bayani: Ambaliyar ruwa: Dabbobi da dama sun mutu a Borno

Tun kafin barkewar wannan cuta ta amai da gudawa a jihar, masana kiwon lafiya har ma da hukumomin kasa da kasa sun yi gargadin bullar cututtuka da dama sakamakon gurbacewar ruwan amfanin yau da kullum da dagwalo bayan ambaliyar ruwa.