1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha ta yi barin bama-bamai a Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou
December 31, 2023

A wani mataki na mayar da martani kan harin da Ukraine ta kai a yankin Belgorod, Rasha ta yi ruwan bama-bamai a yankunan Kharkiv na arewacin Ukraine

https://p.dw.com/p/4ajkJ
Ukraine I Kharkiv I Masu aikin ceto na kokarin kashe gobara, bayan harin Rasha
Ukraine I Kharkiv I Masu aikin ceto na kokarin kashe gobara, bayan harin Rasha Hoto: Yevhen Titov/picture alliance/Anadolu

Rasha ta kaddamar da wasu jerin hare-hare a yankin Kharkiv na arewacin Ukraine, a wani mataki na ramuwar gayya kan mummunann harin nan da Ukraine ta kai wa Rasha a yankin Belgorod, da ya kashe mutane 21, da raunata wasu fiye da 100, Rasha ta bayyana da na ta'addanci.

Hukumomi a Kharkiv, sun ce duk da yake harin na Rasha da jirage maras matuka bai far wa sansanonin ko makaman soja ba, to amma kuma ya illata gijen jama'a da wuraren shakatawa da ofisoshin gwamnati.

Nan gaba a yau ake sa ran daukacin shuwagabannin kasashen biyu na Rasha da Ukraine, su gabatar da jawaban bankwana da shekarar 2023, wanda a ciki ake sa ran Shugaba Zelensky da takwaransa Putin, su bayyana mataki na gaba na yakin da suke gwabzawa.