1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daliban Kagara sun fada hannun masu satar mutane

Uwais Abubakar Idris MAB
February 17, 2021

Wasu ‘yan bindiga sun afka wa makarantar sakandare ta garin Kagara da ke jihar Niger inda suka yi garkuwa da dalibai masu yawa da ma wasu malamai, a yanayin da ke nuna ci gaba da tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3pUB9
Symbolbild Entführung Schüler Nigeria
Hoto: Sunday Alamba/picture-alliance/AP

Da talatainin dare ne ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka afka wa makarantar da ke garin Kagara a daidai lokacin da dalibai ke barci. Sun fara ne da far ma gidan malamai kafin su shiga dakin kwannan dalibai, inda bayan sun tashe su suka sanya su yin layi tare da tasa keyarsu.

Abubakar Baba Umar, jami’in yada labaru na karamar hukumar Rafi wanda Kagara ke a karkashinta a jihar Niger da ke arewacin Najeriya, ya bayyana cewa an kashe dalibi daya, yayin da aka kwashi daliban 26 da kuma malamai da iyalansu. A Takaice dai akalla mutane 42 ne ke hannun masu satar mutanen a halin yanzu.

Akwai dalibai da yawa da suka samu arcewa daga makarantar wadanda suka kwana a cikin daji kafin daga baya su samu isa gidajensu a yanayi na firgici da tashin hankali. Wani dalibi da ya kasance daya daga cikinsu ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda ya ce "bayan da suka tashe su, sun fara bugun mu, mun iso waje sai suka ce mu yi layi. Da muka yi layi, sai suka wace da wasu"

Symbolbild Schüler Nigeria
Wasu daliban sakandaren Kagara sun samud amar arcewaHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture-alliance

Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani Bello ya kammala wani taro kan yanayin tsaro da kwamishinoninsa da 'yan majalisar zartaswarsa, inda ya bayyana cewa babu batun biyan fansa a kokarin da suke yi na maida 'ya'ya ga iyayensu. Duk da hali na sam barka ga iyayen yaran da suka samu ganin ‘yayansu, har yanzu suna cikin yanayi na fargaba da tashin hankali sakamakon abin da ya faru. Malam Harisu Muhammad Isa ya bayyana cewa "ya kamata gwamnati ta yi maganin abin domin kasar Kagara a wargaza ta."

Garin Kagara da ke jihar Niger ya dade yana fuskantar hare-hare na ‘yan bindiga da ke tsallakowa daga yankin Birnin Gwari da kuma jihar Zamfara, inda a 'yan shekarun nan suka yi kaka-gida a dazuzzukan da ke yankin.