Hukumar zaben Najeriya ta bayyana dalilan dage zabe
February 16, 2019Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana dalilai na jinkirin isowar kayan zabe da sauya katunan jefa kuri’a da suka kone a matsayin dalilan da suka sanya dage zaben Najeriya lokacin da shugabanin kungiyoyin fararen hula suka yi Allah wadai da abin da ya faru a game da zaben.
To taro ne dai da shugaban hukumar zaben ya fito fili ya bayyana batu na jinkirin isowar kayan zaben da bayanai suka nuna cewa sai a maraicen Jumma’a aka samu isowar wasu, da kuma sama da katunan jefa kuri’a dubu dari da suka one da dole ne sai an sake yi masu aiki, wanda zai dauki kwanaki biyar.
To sai dai da alamun wakilan jamiyyun basu gamasu da wadanan dalilai ba, kama daga jamiyyar PDP da ta APC. Comrade Adams Oshimole shi ne shugaban jamiyyar APC mai mulki a Najeriya.
Kungiyoyin fararen hula da cikin Najeriya da waje suna nuna damuwar yadda lamarin zai iya shafar sahihancin zaben kansa. Ko wane bayani suke das hi ne a kan wannan batu? Dr Kole Shettima shi ne shugaban majalisar gudanarwa ta kungiyar bunkasa dimukurdiyya da ci gaban kasa.
Jam'iyyar PDP ta ‘yan adawa dai ta turo tawaga mai karfi.