Dambarwar rabon mukamai a majalisar Najeriya
May 12, 2023Kusan daukacin masu takarar shugabancin majalisun biyu sun sa kafa sun shure hukuncin uwar jam'iyyar APC kan ko wanene suke da burin jagorantarsu cikin majalisar ta 10 da ake shirin girkawa.
To sai dai kuma APC ta amsa kuskurenta tare da alwashin sake nazarin rabon mukaman da ta ce babu tuntuba mai nisa kafiin iya kai wa ga fidda su.
Jam'iyyar ta ce tana jiran dawowar shugaban kasar da ke shirin hawa gado, kafin sanin mataki na gaba
Matakin kuma da ke shirin kwantar da hankula tsakanin 'yan majalisar da suka dauki lokaci suna nunin yatsa ga shugabancin na kasa.
Sanata Ali Ndume dai na zaman daya daga cikin masu neman jagorantar majalisar dattawa ta kasar da kuma ya ce akwai alamun rainin wayo, tunanin dora wani bisa ragowar 'yan majalisar da sunan shugabanci na gaba.
Kokarin shawara ko kuma rakumi da akala dai boren masu tsintsiyar dai daga dukkan alamu ya girgiza jiga-jigan jam'iyyar da suka dauki lokaci suna sauraron 'yan tawayen kuma suka dau lalashinsu a yanzu.
Hon Inuwa Garba na zaman dan majalisar wakilan daga Gombe kuma ya ce duk wani kokari na kauce wa doka yana iya jefa majalisun kasar cikin rudani.
Sai dai kuma daga dukkan alamu matakin APC na kama da kokarin jan lokaci maimakon biyan bukata a bangaren masu tsintsiyar da ke cikin halin rudu.
APC dai na tsakanin tabbatar da tsarin karba karba cikin barazanar tawayen 'yan majalisa da kuma kyale mai karfi sai Allah da ke iya karewa da tabbatar da babba da jaka a shugabancin majalisun kasar guda biyu.
Majiyoyi dai sun ce akwai masu tayin dalar Amurka miliyan guda ga kowane dan majalisa a cikin neman shugabancin mai tasiri.