Daukar ciki a makarantu na karuwa a Afirka
November 18, 2021'Yan matan kasashen Afirka na fuskantar matsalar auren wuri da na dole tare da tsautsayin samun juna biyu a lokacin da suke tsakiyar karatu. Wadannan matsaloli na haifar masu da kyama a makarantu ko tsakanin sauran al’umma tare da tauye ‘yancinsu na samun ilimi. Sai dai kasancewar wannan kalubale ya zama ruwan dare a kasashe kamar Kamaru da Ghana da Najeriya, ya sa wani taro kwanaki uku da aka gudanar a birnin Niamye na Jamhuriyar Nijar ya dukafa kan wannan batu don samar da mafita.
kasar Kamaru na daya daga cikin kasashen Afirka da suka haramta wa mata dalibai masu dauke da ciki shiga makarantu, lamarin da ke jefa wadannan 'yan matan da iyayensu cikin damuwa. A Ghana kuwa, bangaren marasa rinjaye na majalisar dokokin kasar ya shawarci gwamnati da ta gaggauta goge tsarin karatu, saboda tsarin na haifar da mummunar sakamako a kan dalibai mata da suke yawaitan daukar ciki a makarantun sakandaren mata