1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Kamaru: Tsawaita wa'adin 'yan majalisar dokoki

Zakari Sadou AH
July 11, 2024

'Yan majalisar dokokin kasar Kamaru sun amince da kudirin dokar kara wadin yan majasalisar dokoki da shugaban kasar Paul Biya ya shigar gaban su ranar Asabar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4iAhC
Hoto: AFP/Getty Images

 Da farko dai wa'adin 'yan majalisar dokokin Kamaru zai zo karshe ranar 10 ga watan Maris 2025 sai shubaban kasa Paul Biya ya kara har zuwa 30 ga watan Maris 2026. Shugaban ya yi hakan ne domin a fifita zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a watan Oktoba 2025.

Karo na uku kenan a jere da Paul Biya ke kara wa'adin yan majalisar kasar

Paul Biya Shugaban Kasar Kamaru
Paul Biya Shugaban Kasar KamaruHoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

Sai dai ba karon fako ba ne da tarihin zabuka na 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi a kasar ke maimaita kansa ba, karo na uku kenan a jere da Paul Biya ke kara wa'adin 'yan majalisar kasar 180 sakamakon rashin ishashen kudi a asusun gwamnati kamar yadda jaridar Cameroun Tribune ta gwamnatin kasar ta sanar a babbar shafinta. Duk da cewa 'yan siyasa bangaren adawa kamar Koupi Adamou ya kalubalanci matakin na Paul Biya wanda a cewarsa, domin hana wasu jam'iyyun adawa shiga zabuka masu  zuwa ne.

Korafin'yan adawa a kan matakin wanda suke sukarsa

DW Premium News | The silenced opposition in Cameroon
Hoto: Blaise Eyong

‘'ba karon farko ba ne da ake kara wa'adin zababbun 'yan majalisar dokoki, amma ina so na ce na wannan shekara na da wani kallo na musamman wanda da alamar neman yi  wa kalandar zaben kasar gyarar fuska domin sanya wasu manyan jam'iyyun adawa cikin mummunar hali ba za mu iya yarda da haka ba, a matsayina na mai kishin kasa kuma mai mutunta  demokaradiyya''