Dokar ta-baci kan fyade a Najeriya
June 12, 2020Talla
A kusan karshen yinin ranar Alhamis ne dai gwamnonin Najeriya 36 suka fitar da matsaya a kan wadanda ke aikata wannan kazamar dabi'a, bayan zanga-zangar da ta karade kasar da ke nuna gajiya da lamarin.
A jawabin da ya yi wa 'yan kasar albarkacin cikar kasar shekaru 21 da kama tafarkin dimukuradiyya, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya kadu matuka da yadda fyade ke karuwa a Najeriyar, musamman na kananan yara mata.
Shi ma ministan shari'ar kasar, Abubakar Malami, ya ce nan ba da jimawa ba za a kaddamar da kwamiti a dukkanin manyan ma'aikatu na gwamnatin tarayya wadanda za su tsara hanyoyin sauya hukunci kan cin zarfin na mata, hukuncin kuma da zai dace da ko'ina a duniya.