1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Dortmund ta gasa wa Brugge aya a hannu a wasan zakarun Turai

Mouhamadou Awal Balarabe
September 19, 2024

Wakiliyar Jamus Borussia Dortmund ta lallasa Club Brugge ta Beljiyam da ci 3-0 ciki har da Kwallaye biyu da Jamie Bynoe-Gittens ya zura, yayin da Manchester City ta Ingila ta tashi 0-0 da Inter Milan ta Italiya.

https://p.dw.com/p/4kolC
Jamie Bynoe-Gittens ya taka rawar gani a nasarar da Dortmund ta yi a kan Brugge
Jamie Bynoe-Gittens ya taka rawar gani a nasarar da Dortmund ta yi a kan BruggeHoto: Leon Kuegeler/REUTERS

Godiya ta tabbata ga dan wasan gaba na Borussia Dortmund Jamie Bynoe-Gittens da ya zura kwallaye biyu a cikin mintuna 15 na karshe a ranar Brugge bayan da aka sanya shi a filin daga, kafin Serhou Guirassy dan asalin Guinea Conakry ​​ya maka bugun fenareti bayan da aka yi karin lokaci, lamarin da ya sa aka tashi Dortmund na da ci uku yayin da Brugge ke nema.

Karin bayani:Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai 

Ita kuwa Paris Saint Germain ta Faransa ta jira har mintuna na karshe kafin ta zura wa Girona kwallon 1-0  da ya sa ta nasara, yayin da Manchester City ta Ingila ta yi kunnen doki da Inter Milan ta Italiya 0-0.  Irin wannan sakamako na 0-0 aka samu a karawa da aka yi tsakanin daya wakiliyar ta Italiya Bologna da Shakhtar Donetsk ta Ukraine, yayin da Sparta Prague ta gasa wa Salzburg aya a hannu da 3-0. A nata bangaren Celtic Glasgow ta yi wa Slovan Bratislava ruwan kwallaye 5-1.

 Bayan wasanni goma sha biyu na makon farko na gasar zakarun Turai, Bayern Munich ce ke kan gaba a yawan zura kwallaye, amma take tafiya kafada da kafada a yawan maki da wasu kungiyoyi tara da suka yi nasara a wasanninsu.

Karin bayani: Bayern ta yi nasara a fitowar farko a Champions League

 A wannan Alhamis ne Monaco za ta karbi bakuncin FC Barcelona  yayin da Atalanta za ta kara da Arsenal ta Ingila. Ita kuwa Atletico za ta kece raini ne RB Leipzig ta Jamus yayin da Brest ta Faransa za ta yi wasanta na farko sabon shiga Sturm Grazda ta kasar Ostiriya.