Duba makomar yankin Arewa maso gabashin Najeriya
January 2, 2017To sai dai kuma tun ba akai ga ko'ina ba tambayoyi suka fara bullowa daga 'yan kasar ta Najeriya game da makomar yankin da ke zaman mafi talauci cikin kasar a halin yanzu. Kama daga 'yan kungiyar da sojoji suka ce sun watsu cikin al'umma ya zuwa ga masu tururuwa ta komawa zuwa gida a yankin na arewa maso Gabas dai, daga dukkan alamu har yanzu da sauran tafiya kan hanya ta tsake tabbatar da komawar lamura dai dai a wannan yanki. Tsananin talauci da ke da ruwa da tsaki da janyewar tafkin Chadi na zaman wata babbar matsala, baya ma ga rikicin na Boko Haram da ya raba miliyoyi mutane da muhallinsu.
Wasa da rayuwa saboda siyasa ko kuma jahilci na mazauna yankunan, ko bayan sake zama na lafiyar dai akwai kuma tsroron nisa ta akidar da ta kai ga haihuwar Boko Haram, na iya jawo matsala ga kokari na daidaiton lamura a nan gaba. Jajircewa kan wannan ne dai ake ta'llakawa da yaduwa dama tasiri na rikicin Tatsine a shekaru 30 da doriya can baya, abun da ya sanya kallon tsaf ga makomar yankin ka zama na wajibi akan hanyar komawar lamura dai dai.
ya zuwa yanzu dai yakin kasar ta Najeriya na tunkahon nasarar ne bisa karfi na tuwo sakamakon jajircewar sojojin da sukai nasarar kwato Camp Zairo da ke zaman matattara ta 'yan ta'adda. Ana kuma kallon rushewar tsari na bangarorin tattara bayanai na da ruwa da tsaki da sulalewar da dama daga shugabannin kungiyar ta Boko Haram ya zuwa 'yar boye tare da sabon bidiyon da ya nemi rushe ikirarin sojojin kasar ta Najeriya. Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a kokari na tabbatar da lafiya a cikin yankin da ya kai ga kisa na maciji amma kuma har yanzu yake kallon kansa yana reto.