Ebola a Legas - Rayuwa cikin fargaba
Najeriya ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, kuma birnin Legas mai mazauna miliyoyin mutane, ita ce cibiyar hada-hadar kasuwanci a kasar. A cikin watan Yuli cutar Ebola ta farko ta bulla a birnin.
Gwajin zafin jiki kafin a shiga shago a yi sayayya
Jami'ai na gwajin zafin jiki a gaban kofar shiga kantuna. Yanzu wannan matakin an saba da shi a shaguna da dama a Legas, duk da cewa ba a samu sabon labarin harbuwa da kwayoyin cutar Ebola a birnin ba. Sai dai duk da haka barkewar Ebola ta sa akasari mazauna birnin suna takatsantsan.
Birni na miliyoyin mutane a cikin hatsari
Kimanin mutane miliyan 21 ke zaune a Legas, birni mafi girma a Afirka. Masana sun yi gargadi cewa kwayar cutar ka iya yaduwa cikin sauri a birnin mai cunkoson jama'a. "Ku yi tunani abin da zai faru, idan wani kwandasta a cikin karamar motar safa ya harbu da Ebola…", a cewar wani mai amfani da Twitter wanda kuma ya damu da abin da ka iya faruwa.
"Babu dalilin fargaba"
Hukumomi sun sha kan lamarin, inji Yewande Animashaun-Adeshina lokacin wata ziyara a asibitin yankin Mainland. A wurin ake jinya dukkan masu dauke cutar Ebola na birnin. Mai ba wa gwamnatin jihar Legas shawara kan kiwon lafiya ta damu cewa da yawa daga cikin ma'aikatan asibitin za su ki kula da wadanda suka harbu da kwayoyin Ebola.
Kwayar cuta mai kisa a wurin aiki
"Kwarai kuwa muna cikin fargaba a nan, ko tantama babu", inji Esther Oduwole. Ita ke dafa wa marasa lafiya na Ebola abinci, tana kuma kula da su. Ta ce da yawa daga cikin ma'akatan asibitin sun ki zuwa aiki bayan an kwantar da majinyaci na farko da ya harbu da cutar Ebola.
Samar da bayanai godiya ga lambobin Hotline
Akwai masu aikin sa kai don yaki da Ebola. Hubaidat Olawunmi Tobun daliba mai koyon aikin likita tana amsa wayoyi kusan 70 a kowace rana ta lambar wayoyin da ake bugawa kyauta. Tana kuma ba da shawara ga 'yan Najeriya. "Kasata na bukata ta yanzu", inji dalibar mai shekaru 25. "Ina yi wa mutane bayani game da cutar."
Bokaye, jita-jita da wadanda Allah Ya zaba
Samar da bayanai na da muhimmanci domin an yarda da canfi. Alal misali Fasto Golden Ozor ya dafa wani tsimi a cocinsa da ke wajen Legas, wanda ya ce yana ba da kariya daga Ebola. "Allah Ya sanar da ni mahadin tsimin wanda kuma zan rarraba shi a fadin kasar nan" inji limanin cocin. Mabiyansa su 20 ne suka fara gwada tsimin.
Wanke hannu maimakon canfi
A daura da cocin Emmanuel Abioli ya tsaya a gaban shagonsa yana girgiza kai saboda mamaki. "Ko shakka babu Ebola na da hatsari, domin har yanzu ba ta da allurar rigakafi", inji matashin. Ya fi dogaro da matakan kariya mafi sauki kuma mafi muhimmanci ga kwayar cutar mai kisa: wato yawaita wanke hannu da sabulu.
Jita-jita mai kisa
Mai shago da ke kusa tana tinkarar lamarin a wata hanya ta dabam. "Ai babu cutar Ebola", inji ta. "In ma akwai ta, ai wadanda ba su yi imani ba za ta kama." Camfi da ya yadu a yammacin Afirka babbar matsala ne ga yaki da Ebola. A lokacin da a Najeriya aka yada jita-jitar cewa ruwan gishiri na ba da kariya daga kwayar cutar, mutane biyu sun mutu saboda amfani da ruwan gishiri fiye da kima.
Sako daga 'yan kasa
Saboda haka mahukunta suka lillika sanarwa a duk fadin birnin, kamar nan a gaban wani gidan cin abinci na Fast-Food. Gwamnatin Legas ta fi ba da fifiko da yaki da kwayar Ebola. Shugaba Goodluck Jonathan ya ware karin Euro miliyan tara daga kasafin kudin kasa don tinkarar cutar.
Zama cikin shirin ko takwana a filin jirgin sama
A cikin watan Yuli wani Ba-Amirke dan asalin kasar Liberiya ya kai Ebola Najeriya. A cikin tsananin rashin lafiya ya sauka filin jirgin saman birnin Legas, ya mutu daga bisani. Wadanda suka harbu da cutar sun yi alaka da shi kai tsaye ko ta kan wasu. Duniya ta yaba wa mahukuntan Najeriya domin cikin gajeren lokaci sun gano mutanen kana sun kebesu.
Ko shin an koyi darasi?
Najeriya na fatan magance yaduwar kwayar cikin gaggawa. Tuni dai ta yi mata illa. "Masu zuba jari na tsoron zuwa kasar, dakuna a otel sun kasance wayam" inji dan kasuwa Kasumu Garda. Sai dai kasar ta koyi abubuwa da yawa saboda barazanar cutar. "Mun hada kai gaba daya don magance matsalar - wannan ya kamata ya zama matakinmu na yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram", inji Garda.