Ebola ta kashe wani likita a Rivers
August 28, 2014Hukumar Lafiya ta Duniya WHO dai ta ce babu tabbacin cewar likitan da ya mutu a jihar Rivers da ke Tarayyar Najeriya ya mutu ne sakamakon cutar Ebola. Hukumar ta shaidawa manema labarai a cibiyarta da ke a Geneva cewar tuni jami'anta suka tafi Fatakwal babban birnin jihar ta Rivers domin haƙiƙance dalilin mutuwar tasa. Tun da fari dai ministan kiwon lafiya naNajeriya Onyebuchi Chukwu ya sanar da cewar likitan ya mutu ne bayan da ya duba wani wanda ya yi mu'ammala da ɗan ƙasar Laberiyan nan Patrik Sawyer da ya kai wa Najeriyar tsabara Ebolan. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ya zuwa Talatar wannan mako yawan mutanen da suka hallaka sakamakon cutar Ebola a ƙasashen Gini da Laberiya da Saliyo da kuma Najeriya ya kai 1,552, yayin da kawo yanzu yawan waɗanda aka keɓe saboda an tabbatar da cewa sun kamu da cutar ta Ebola mai saurin kisa ya kai sama da 3000, inda ta ce yawan waɗanda suka kamu da cutar ka iya kai 20,000.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane