Ebola tana ci gaba da kisa
September 10, 2014Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa ana samun karuwar mutanen da suka kamu da cutar Ebola cikin kasashen yankin yammacin Afirka. A cikin wata sanarwa ta wannan Talata da ta gabata, hukumar ta ce kusan mutane dubu-uku cutar ta hallaka, daga cikin mutanen kimanin 4300 da suka kamu da cutar ta Ebola, a kasashen Gini, da Laberiya, da Saliyo, da Najeriya, da kuma Senegal da aka samu wani mai dauke da cutar.
Tuni kasashen Amirka, da Birtaniya, da kuma Faransa suka dauki matakin tura jami'in kiwon lafiya domin taimaka wa kasashen da aka samu annobar cutar ta Ebola.
Jami'in MDD da ke kasar Laberiya Karen Landgren ya ce Ebola tana yaduwa kasar wutar daji a kasar. Ministan tsaron kasar ta Labariya Brownie Samukai ya ce cutar Ebola tana bazara wa ci gaba da dorewar kasar da ke yankin yammacin.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu