1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS na shirin yaki da Boko Haram

January 17, 2015

A mako mai zuwa neshugabannin kasashen yammacin Afirka za su tambayi izini ga kungiyar Tarayyar Afirka domin kafa wata runduna ta musamman da za ta yaki 'yan kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1EM1F
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Wannan labari ya fito ne daga Shugaban kasar Ghana John Mahama yayin da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, inda ya kara da cewa wannan runduna ita ce za ta kasance wata amsa ga wannan kungiya da ta kashe dubunnan mutane a Tarayyar Najeriya, wadda kuma har ta fara kai hare-harenta a yankin kasashen Kamarun da ma Jamhuriyar Nijar. A cewar shugaban kasar ta Ghana, wannan kungiyar mai membobi a kasashen Somaliya, da Kenya, da Mali da ma wasu wurare, ta kasance babbar annobar da ala tilas a tashi tsaye kan ta don ganin bata cimma gurin da ta sa ma gaba ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal