1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar kungiyar ECOWAS ga Mali

December 13, 2021

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, ta yi barazanar kara saka takunkumi kan mahukuntan mulkin sojan Mali.

https://p.dw.com/p/44CtG
Nigeria | ECOWAS Gipfel
Kungiyar ECOWAS ta yi barazana ga MaliHoto: Präsidentschaft von Niger

Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta nunar da caewa muddun gwamnatin mulkin sojan ta Mali ta gaza nuna aniya ta zahiri kan mayar da kasar kan tafarkin dimukaradiyya cikin makonni masu zuwa, tabbas za ta sanya sabon takunkumi. Yayin taronsu karo na 60 a birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya, shugabannin kasashen kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamman, sun bai wa gwamnatin Mali wa'adin zuwa karshen wannan wata na Disamba da muke ciki, domin su fitar da jadawalin zabe kamar yadda mahukuntan kasar suka yi alkawari lokacin da Kanar Assimi Goita ya kwace madafun iko. A watan Mayun wannan shekara ne dai, Kanar Assimi Goita ya yi juyin mulki karo na biyu tare da nada kansa a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi. Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO dai na bukatar a shirya zabuka a watan Fabarairuna shekara mai zuwa ta 2022, kamar yadda sojoji suka yi alkawari lokacin da suka kwace madafun iko amma kuma yanzu suke jan kafa.

Mali Oberst Assimi Goita, Anführer der malischen Militärjunta
Jagoran mulkin soja na kasar Mali, Kanar Assimi GoitaHoto: Francis Kokoroko/File Photo/Reuters

ECOWAS din ta ce muddun sojojin da ke mulkin Mali suka gaza kan wannan alkawari, babu gudu babu ja da baya za a saka musu takunkumi. Addina Karembe na gamayyar ASMA CFP yana da yakinin cewa sojojin da ke rike da madafun ikon kasar ta Mali, suna wasa da hankalin mutane wajen neman tattaunawa ta kasa maimako tsara jadawalin zabe. Muddin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamman ECOWA ko CEDEAO ta kakaba takunkumin, zai shafi fannonin tattalin arziki da kudin kasar ta Mali daga ranar daya ga watan Janairun shekara ta 2022 da ke tafe. Mai shiga tsakani kan rikicin na Mali kana tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai kai ziyara birnin Bamako fadar gwamnatin kasar a kwanaki masu zuwa, domin tattauna yanayin da ake ciki da mahukuntan gwamnatin wucin gadin.