1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayin ECOWAS ko CEDEAO kan Mali

May 27, 2021

A yayin da ake ci gaba da kace-nace bisa makoma ta kasar Mali, kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma ta sa kafa ta shure ajiye aikin shugaban kasar ta Mali Bah Ndaw da firaministansa Moctar Ouane.

https://p.dw.com/p/3u4pQ
Nigeria Abuja | Militärputsch ECOWAS | Buhari und Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Media Department Präsidentiell Villa Abuja Nigeria

Wata ganawa sirri a tsakanin shugaban Ghana Nana Addo Akufo-Addo kana shugaban kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS ko CEDEAO da mai masaukin baki kuma shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ta kammala a Abuja, inda shugabannin guda biyu suka mayar da hankali bisa rikicin kasar ta Mali da ma rikicin kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Duk da sakin manyan jami'an gwamnatin kasar Mali biyu dai, ECOWAS din ta ce ba ta karbi ajiye aikin na shugaba Bah Ndaw da kuma Firaminista Moctar Ouane ba. Ajiye aikin dai a fadar shugabannin na kasashen yankin yammacin Afirkan, na zaman tursasawa daga sojojin Bamakon, abun kuma da kasashen suka ce ba ta sabu wa.

Karin Bayani: Za a kafa gwamnatin rikon kwarya

Ministan harkokin wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama ya ce matsayin ECOWAS din shi ne ganin an mayar da su kan kujerun mukamansu ba tare da bata lokaci ba, inda ya ce abin da ya faru a kasar Mali na zaman juyin mulki da kuma ya saba da ka'idojin kasashen yankin: "ECOWAS na tuntubar shugaban juyin mulkin, domin a zahiri juyin mulki ne a cikin juyin mulk. Lallai an ce shugaban kasar da firaministansa sun  sanar da ajiye aiki, amma mu a ganinmu tilasta su aka yi. Saboda ba zaka ce mutum ya ajiye aiki a lokacin da yake tsare ba. Matsayinmu shi ne a koma bisa tsarin da ake. ECOWAS na bin rikicin sannu a hankali. Tsohon shugaban Najeriya shi ne yake shiga tsakani da tattaunawa. Haka kuma shugaban Ghana shi ne jagoran ECOWAS, shi ma kuma na tuntuba ta kai tsaye da su. Saboda haka zamu ga mai shugabannin juyin mulkin ke so, ko sun shirya bayar da hadin kai ko a a kafin sanin mataki na gaba da ya kamata mu dauka."

Guinea-Bissau Delegation ECOWAS
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey OnyeamaHoto: DW/B. Darame

To sai dai kuma in har kasashen yankin na shirin sanya kafa guda ta wando a tsakaninsu da sojojin na Mali dai, manyan kasashen kungiyar biyu wato Ghana da Tarayyar Najeriyar dai, sunce sun yi nisa wajen warware rikicin cinikin da ya nemi farraka dangantaka ta kasashen biyu. Kasar ta Ghana dai ta sanya harajin dala Miliyan daya ga duk wani bakon da ke da bukatar kasuwanci a kasar. Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fara nuna alamun tsami, tun bayan rufe iyakar Najeriyar da makwabta. Ghana dai na zaman daya a cikin manyan kawayen kasuwancin Najeriyar a cikin yankin yammacin Afirka.

Karin Bayani: Dangantakar Najeriya da Ghana na shirin yin tsami

A ranar Litinin da ke tafe ne dai, wata tawagar Najeriyar ke shirin isa birnin Accra da nufin tattaunawa kan batun da ya tayar da hankula can baya. Niyi Adebayo na zaman ministan ciniki da kasuwanci na Najeriyar da kuma zai jagoranci tawagar mai tasiri: "A gaba daya babban burin tawagar mu na zaman tunkarar mahukuntan Ghanan, kan  wariyar da ake nunawa yan kasuwar mu dake can. Muna samun korafi da yawan gaske daga yan kasarmu da ke Ghana kan irin matsayin  kasar  akan su. Za mu je mu tattauna a madadin tarrayar najeriya da kuma madadin yan kasarmu dake can mu ga hanyar da zamu bi domin warware matsalar. Za mu zauna dasu zamu tattauna batun da su kuma za mu samo hanyar da zata amfani bangarorin guda biyu.  tattauna A baya mun gana dasu, sun turo wakilansu Abuja mun kuma dauki lokaci muna tattaunawa, kuma wannan  ziyara ta mai da martani ce a garesu, domin ganin mun iya aiwatar da abubuwan da muka amince."