ECOWAS ta ji zafin rashin mambobinta uku
July 8, 2024Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirka ECOWAS, ta ce ta ji takaicin rashin nasarar samun daidaitawa tsakaninta da gwamnatocin soja da ke mulki a kasashen Burkina Faso da Mali gami da Jamhuriyar Nijar, wadanda duk suka tabbatar da ballewarsu a karshen mako.
A cewar kungiyar ta ECOWAS za ta ci gaba da kara himma bil hakki domin ganin sun sasanta da kasashen uku.
A jiya Lahadi, an jiyo shugaban hukumar ECOWAS din Oumar Touray na fada lokacin taron da suka yi a Abuja babban birnin Najeriya, cewa yankin yammacin na Afirka na fuskantar barazanar rabuwa da kuma karuwar hadari na rashin tsaro a halin yanzun.
Oumar Touray ya ce 'yancin zirga-zirga da kasuwanci tsakanin mutum miliyan 400 na kasashen kungiyar mai shekaru 50 da kafuwa na fuskantar barazana.
Tuni dai kasashen uku wato Burkina Faso da Mali da Nijar din suka girka kawancensu na kasashen Sahel uku da aka yi wa lakabi da AES.