1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali da Nijar da Burkina sun juya wa ECOWAS baya

Abdoulaye Mamane Amadou Abdulkarim Muhammad(Salissou Boukari)
July 6, 2024

Kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun kammala taron koli na farko a karkashin jagorancin kungiyar AES, shugabannin kasashen sun zabi Assimi Goita na Mali a matsayin shugabanta na farko kan wa'adin shekara daya.

https://p.dw.com/p/4hxUF
Shugaba  Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina Faso
Shugaba Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina FasoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Shugabannin uku bayan da suka jajanta wa al'ummar kasashensu kan mace-macen da ayyukan ta'addanci ke haddasawa, sun nuna jajircewarsu tare da cigaba da yakar kungiyoyin masu da'awar jihadi a yankin Sahel.

A karon farko, kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da suka kwace mulki da tsinin bindiga daga hannun farar hula sun yi taron koli a karkashin kungiyar kawance ta AES.

Karin bayani : Shugabannin Nijar da Mali da Burkina Faso na taro

Shugabannin sun kafa kungiyar kawancen yankin Sahel wato AES  bayan fice wa daga ECOWAS  sakamakon dakatar da su daga harkokin kungiyar. Dama dai kasashen sun yanke alaka da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa, inda suka karkata alakarsu da kasar Rasha.

'Yan Nijar na yaba huldar kasarsu da ta Rasha
'Yan Nijar na yaba huldar kasarsu da ta RashaHoto: AFP/Getty Images

Karin bayani: Shugaban Nijar na ziyarar aiki a Mali da Burkina Faso

Mahalarta taron kolin na Nijar sun rattaba hannu kan yarjejenioyin bunkasa tattalin arziki da shige da fice da tsaro da inganta hulda a tsakaninsu ta fannoni da dama.

Karin bayani : Nijar: Amurka za ta kammala janye sojojinta

Shugabannin kasashen uku sun zabi shugaban kasar Mali a matsayin shugaban gamayyar kungiyar ta AES a tsawon shekara daya, sannan kasar Burkina Faso za ta karbi bakuncin taro na gaba da shugabannin za su halarta, a gefe guda, shugabannin kungiyar ECOWAS za su gudanar da taron koli a Najeriya a ranar Lahadi.