EFCC da Interpol na kokarin hana zamba
August 2, 2016Diran mikiyar da aka yi wa wannan mutumin mai kimanin shekaru 40 da haihuwa da ya yi kwance-kwance ya tafka zamba ta kafar yanar gizon daga Najeriya ya kasance abin da ya daga hankalin masu yaki da wannan mumunan dabi'a. Bayanai sun tabbatar da cewa mutumin da hukumar ta bayyana shi da suna Mike ya na da aiki ne da gungun mutane kusan 40 a Najeriya da Malaysia da ma Afrika ta Kudu.
EFCC dai ta yi wannan kamu ne tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol, inda suka gano otal din da mutumin ke zaune a garin Fatakwal na jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya. Mr. Wilson Uwujaren da ke zaman kakkin hukumar ta EFCC ya bayyana wa DW cewar ''muhimmancin kamen da muka yi shi ne sakon da ya ke aikawa wato duk inda ka ke to hukumar na da karfi kaiwa gareka''.
Fiye da shekara guda kenan da Najeriya ta samu kafa dokar yaki da masu wannan dabi'a ta yin zamba ta hanyar amfani da yanar gizo wadda ta bada dama ta gabatar da shaidu na yanar gizo a kotu domin tuhumar masu irin wannan laifi. EFCC din dai ta ce wannan doka ta taimaka domin ta bada karfin iko na aiki inda ake samun bakado masu zamba ta yanar gizo don hukunta su a kotu.
Ko da ya ke hukumar ba ta yi karin bayani a kan halin da ake ciki da bincike a kan lamarin ba, amma dai ta ce kame Mike ta hanyar amfani da na'urorin zamani ta yadda aka bi sawunsa har dakin otal dinsa a Fatakwal na nuna a zahiri cewa masu irin wannan hallaye ba su da wurin boyo.