EFCC ta kama Rochas Okorocha a Abuja
May 25, 2022Sama da sa'o'i bakwai jami'an hukumar mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta EFCC suka kwashe, suna wasan mage da bera tsakanin su da tsohon gwamnan na jihar na Imo Rochas Okorocha a gidansa da ke unguwar masu hannun da shuni na Maitama da ke Abuja, abin da ya kai su ga kutsa kai a cikin gidan da ma harbin iska a sama kafin cafke shi kamar haka.
Ita dai hukumar ta EFCC tana zargin ya tsallake belin da ta ba shi ne kuma duk gayyatar da ta yi masa don bayyana a kotu ya ki, inda kotun ta ce in har ba ta gabatar da shi ba a ranar 30 ga watan nan to za a yi watsi da shari'ar.
Hukumar EFCC dai na zargin Sanata Rochas Okorocha ne da cin hanci da rahsawa da zambar kudade ta Naira biliyan biyu da dubu 900, zargin da suka dade suna kulle kurciya a tsakaninsa da hukumar, domin a baya an kai shi kotu amma kotun ta wanke shi.
Shi dai Sanata Rochas Okorocha ya kaiga roko da ban baki a kan kawanyar da jami'an suka yi a gidansa a lokacin da ya yi wa ‘yan jarida jawabin halin da yake ciki.
Amma ga Barrister Mainasara Umar masani a fanin shari'a ya bayyana muhimmanci kara kaimi a kan wadanda ake zargi a kokari na tsarkake al'amura.
Kamun kazar kuku da hukumar ta yi wa Sanata Rochas Okorocha na iya sanya ya rasa kokari na takarar shugabancin Najeriya a karkashin jamiyyar APC, koda yake a baya an ga yadda wadanda ke tsare a gidan yari ke tsayawa takara da ma cin zabe a Najeriyar.