1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari birnin Ankara na Turkiyya

October 1, 2023

Rahotanni daga Ankara, babban birnin Turkiyya sun yi nuni da cewa an kai wani hari bam a kusa da gine-ginen majalisar dokokin kasar da kuma ma'aikatar cikin gida.

https://p.dw.com/p/4X1Fc
Wurin da aka kai harin bam a Ankara
Wurin da aka kai harin bam a AnkaraHoto: Cagla Gurdogan/REUTERS

Rahotannin sun kuma nuna cewa harin ya rutsa da guda daga cikin maharan. Kafofin yada labaran Turkiyya sun ruwaito cewa an jiyo karar harbin bindiga a wurin da aka kai harin.

Harin dai ya auku ne a lokacin da ake dab da dawowa zaman majalisa domin sauraran jawabin shugaba Recep Tayyip Erdogan, da ka iya kasancewa gwamnatin Ankarar ta amince wa kasar Sweden zama mamba a kungiyar kawance ta NATO.

Karin bayani: Matakan shigar Sweden NATO daga Turkiyya

Babban daractan ma'aikatar cikin gida na kasar Ali Yerlika ya ce, maharan sun yi amfani da abun hawa ne wajen yunkurin kai harin a kofar ginin ma'aikatar.

A jawabinsa a wannan Lahadin, shugaba Erdogan ya yi Allah wadai da harin. Ya ce wadanda ke da hannu a harin ba za su cimma burinsa na wargaza zaman lafiya da kuma tsaron kasar ba. Tuni aka fara gudanar da bincike kan hari kana aka tsaurara matakan tsaro a birnin.