1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

EU na duba yiwuwar rage wa Chaina harajin shigar da hajoji

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 22, 2024

Ministan harkokin tattalin arzikin Jamus Robert Habeck ne ya bayyana hakan a Shanghai

https://p.dw.com/p/4hO3R
Hoto: Sebastian Gollnow/dpa/picture alliance

Ministan harkokin tattalin arzikin Jamus Robert Habeck, ya shaidawa Chaina cewa kofar kungiyar tarayyar Turai EU a bude take, wajen tattaunawa tare da nazartar harajin shigar da hajojin Chainan cikin Turai.

Karin bayani:Chaina da Jamus: Karfafa alaka kan yanayi

Mr Habeck da ke ziyarar aiki a Chaina, ya bayyana hakan ranar Asabar a Shanghai, bayan da ya zama babban jami'in EU na farko da ya ziyarci Chaina, tun bayan kakaba mata tarin haraji da EU ta yi, kan motocin da take kerewa masu amfani da lantarki.

Karin bayani:Sin ta saka wa wasu kasashen EU takunkumi

Ya kara da cewa daga nan zuwan watan Nuwamba mai zuwa, komai ka iya faruwa na yarjejeniyar EU da Chaina kan harajin, ko da yake suna goyon bayan bayar da dama ga kowa a fagen kasuwancin duniya, amma akwai wasu wurare da ke bukatar daidaita al'amura.