1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Babu wata alakar dunkulewar jini da AstraZeneca

Ahmed Salisu AMA
March 16, 2021

Hukumar kula da ingancin magunguna ta Kungiyar Tarayyar Turai ta ce rigakafin AstraZeneca baya haifar da dunkulewar jini a daidai lokacin da kasashe da dama suka dakatar da ita saboda fargabar fuskantar matsaloli.

https://p.dw.com/p/3qi15
Deutschland Coronavirus l Impfstart bei der Polizei in Rheinland-Pfalz
Alluran rigakafin corona na kamfanin AstraZenecaHoto: Andreas Arnold/dpa/picture alliance

Kasashe da dama na duniya ciki kuwa har da Jamus ne suka dakatar da amfani da rigakafin na Oxford-AstraZeneca bayan da aka fara nuna shakku game da   sahihancin rigakafin musamman ma da yake wasu daga cikin wandan aka yi wa rigakafin sun fuskanci matsala ta dunkulewar jini ya yin da wasunsu suka rasu, sai dai duk da shakku da ma fargaba da ake ci gaba da nunawa kan wannan lamari, shugabar hukumar kula da sahhancin magunguna ta Kungiyar EU ta ce ba wata alama da da ke nuna cewar rigakafin an AstraZeneca ne ya haifar da matsalar ta dunkulewar jini ga wasu daga cikin wadanda aka yi wa rigakafin.

Sai dai duka da wannan, shugabar hukumar Emer Cooke ta ce tuni suka zurfafa bincike kan wandan ake cewar sun samu matsala bayan karbar rigakafin kuma suna sa ran samun cikakken sakamako na bincike da suka kaddamar a ranar Alhamis din da ke tafe, yayin da a share guda ta ce irin alfanun da rigakafin ke da shi wajen kare al'umma daga kamuwa da cutar corona ya sha gaban irin matsalolin da ka iya tasowa.

Karin Bayani: Matakin biyan diyyar corona ka iya karfafa guiwar jama'a

Ga alama wannan ne ya sanya wasu kasashen na nahiyar Turai ciki kuwa har da Beljiyam yanke shawarar ci gaba da amfani da rigakafin kamar yadda kakakin kwamitin kar ta kwana yaki da corona a kasar Yves Van Laetham ya ke cewa "Beljiyam ta yanke shawar ci gaba da amfani da rigakafin AstraZeneca kamar yadda ta fara tun da da fari. Yin hakan na da muhimmanci musamman ma dai idan aka yi la'akari da irin bayanai na kimiyya da aka samar. Muna son kasancewa cikin wadanda za su ci gaba da bin wadannan bayanai na kimiya sau da kafa duk da irin kai-komo da ma zantuka da ake a kafafen watsa labarai da kuma irin siyasar da ta kunno kai kan wannan batu a nan Turai."

Ba hujjar cewa rigakafin na da alaka da dunkulewar jini

Karikatur | Nigeria Covid-19 Impfungen
Hoton barkwanci na rigakafin coronaHoto: Abdulkareem Baba Aminu

Ita ma dai Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da shi kansa kamfanin na AstraZeneca na kan godabe guda da hukumar kula da ingancin magnguna ta Turai game da ingancin rigakafin, kana sun ce ba wata hujja kawo yanzu da aka kafa da ke nuni da cewar rigakafin na da alaka da dunkulewar jini da wasu mutane suka samu a wasu kasashen musamman ma inda aka yi la'akari da yawan wadandan suka samu matsalar wanda ba su taka kara sun karya ba idan aka kwatanta da miliyoyin mutane da aka rigaya aka yi wa rigakafin. Wasu kwararru musamman wadandan ke bincike kan harhada magunguna da kuma na cutuka masu yaduwa na da irin wannan ra'ayi, inda wasunsu ke ganin an sanya siyasa ne kawai cikin sha'anin rigakafin na AstraZeneca.

Karin Bayani: Mace aka fara yi wa rigakafin corona a duniya

Symbolbild Injektionsflasche mit Spritze AstraZeneca
Rigakafin AstraZenecaHoto: Christian Ohde/CHROMORANGE/picture alliance

Dr. Micheal Head na jami'ar Southampton da ke Birtaniya na daga cikin amsu wannan tunani inda ya ce "Irin yadda ake magana kan rigakafin AstraZeneca da ma yadda siyasa ta shiga sha'anin na ban mamaki. A sanina rgakafin yana da kyau sosai kuma inagancinsa kwatankwacin na Pfizer da Moderna ne. Ba shi da wata illa don haka ban ga dalilin da zai sanya mutane su ki amincewa da shi ba, ban kuma san dalilin da zai sanya a ya kasance a sahun gaba ba a cikin batutuwa na siyasa da ake tattaunawa a kai ba." 

Karin Bayani: COVID-19: Sabuwar dokar corona a Najeriya

Duk da irin tabbaci da masana irin su Dr. Head da WHO  da ma hukumar kula da ingancin magunuguna ta Kungiyar EU ke badawa kan ingancin rigakafin, wasu kasashen ciki har da manaya a nan nahiyar Turai na ci gaba da nuna shakku kan rigakafin duk kuwa da cewar an yi wa miliyoyin mutane allurar ba kuma tare da an samu wata gagarumar matsala ba musamma ma a Birtaniya inda nan ne aka mafin yawan mutanen da aka yi wa rigakafin AstraZeneca.